Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyya mai mulki a Kamaru ta ce ana bukatar sama da dala biliyan 5 wajen sake gina yankin kasar mai amfani da turancin Ingilishi
2019-10-19 16:23:07        cri
Jam'iyya mai mulkin Kamaru, CPDM, ta ce kasar na bukatar sama da dala biliyan 5, domin sake ginawa da raya yankuna masu fama da rikici na arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar, dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi.

Kakakin Jam'iyyar Jacques Fame Ndongo, wanda kuma shi ne Ministan kasar mai kula da ilimin gaba da sakandare, ya ce, za a yi amfani da kudin wajen sake gina ababen more rayuwa da 'yan aware suka lalata.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, kudin da kasar ke da su ba za su isa sake gina dukkan kayayyakin more rayuwa da aka lalata ba, amma shugaban kasar ya yi alkawarin farfado da yankunan, kuma zai cika alkawarinsa.

A ranar Alhamis ne Jam'iyyar ta bayyana, yayin wani taron manema labarai cewa, shugaban kasar Paul Biya, ya kuduri niyyar samar da dawwammiyar mafita ga matsalar tsaro a yankunan, tana mai bayyana babban taron kasar da aka yi a farkon watan da nufin kawo karshen rikicin, a matsayin muhimmin lokaci na hadin kai ga kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China