Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru ta jinjinawa tallafin kasar Sin na gina sabon zauren majalissar dokokin kasar
2019-11-13 10:21:12        cri
Kakamin majalissar dokokin kasar Kamaru Cavaye Yeguie Djibril, ya jinjinawa tallafin kasar Sin, na samar da kudade, da gudanar da aikin ginin sabon zauren majalissar dokokin kasar.

Mr. Djibril ya yi wannan tsokaci ne, yayin bude zaman majalissar na watan Nuwambar nan, a jiya Talata a birnin Yaounde. Yana mai cewa matakin na kara jaddada kyakkyawan kawance, da zumuncin dake tsakanin Sin da kasar Kamaru. Ya ce ginin majalissar dokokin zai kara karfafa alakar kasashen biyu, wadda tuni ke cikin kyakkyawan yanayi, dake haifar da moriya ga sassan biyu. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China