Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya bukaci kada a yi kasa a gwiwa wajen yaki da cutar kanjamau
2019-11-30 20:31:53        cri
Gabanin ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya dake gudana ranar 1 ga watan Disamban kowacce shekara, Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da kada a yi kasa a gwiwa wajen daukar matakan kariya da yaki da manyan cututtuka masu yaduwa kamar kanjamau.

Li Keqiang, wanda kuma mamba ne na kwamitin gudanarwa na hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya ta JKS, ya ce kasar Sin ta samu nasarori a fannonin kariya da yaki da cutar kanjamau, yayin da take fuskantar wasu sabbin abubuwa masu jan hankali. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China