Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya bukaci kara zage damtse wajen bunkasa tattalin arziki da rayuwar Sinawa
2019-11-15 10:57:34        cri
A jiya Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci kara zage damtse wajen bunkasa tattalin arziki, da inganta rayuwar Sinawa. Mr. Li Li Keqiang, ya yi wannan kira ne a birnin Nanchang dake lardin Jiangxi, yayin da yake jagorantar wani taron musayar ra'ayi tsakanin masu ruwa da tsaki. Ya ce ya kamata a yi aiki bisa hangen nesa, tare da la'akari da yanayin da ake ciki a wuraren da ake aiwatar da manufofi.

Firaministan na Sin ya kara da cewa, tun daga farkon shekarar bana, Sin ta ci gaba da bunkasa tattalin arzikin ta cikin madaidaicin yanayi, duk kuwa da yanayi mai sarkakiya da kalubale da ake fuskanta.

Game da kalubale da ke shafar ci gaban tattalin arzikin kasar na cikin gida, Li ya yi kira ga mahukunta a kananan matakai, da su ba da gudummawa ta daidaita ci gaban tattalin arziki, matakin da zai kafa kakkarfan ginshikin ci gaba mai ma'ana ga kasar baki daya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China