Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya yi kira da a samar da matakan raya tattalin arziki da jin dadin jama'a
2019-11-26 20:25:12        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar bullo da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 a manyan matakai, tare da bullo da wani sabon mataki na raya tattalin arziki da inganta rayuwar jama'a.

Mr Li ya bayyana haka ne, yayin taron musamman game da shirye-shiryen taron shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 kan raya tattalin arziki da jin dadin jama'a da ya jagoranta jiya Litinin.

Ya ce, kamata ya yi a nazarci tare da kaddamar da wasu manyan manufofi, da manyan matakan gyare-gyare da bude kofa da manyan ayyukan injiniya, don taimakawa shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, da mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki, bunkasa masana'antu da inganta rayuwar jama'a, da kare aukuwa da ma daidaita hadurra. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China