Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya gana da jagororin cibiyoyin kudade na kasa da kasa yayin taron tattalin arziki
2019-11-21 20:30:46        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da jagororin manyan cibiyoyin kudi da tattalin arziki na kasa da kasa 6, yayin taron tattalin arziki da ya gudana a Alhamis din nan.

Jagororin sun hada da shugaban bankin duniya David Malpass, da babban daraktan asusun samar da kudade Kristalina Georgieva, da mataimakin babban daraktan kungiyar cinikayya ta duniya WTO Alan Wolff. Sauran sun hada da babban daraktan kungiyar kwadago ta kasa da kasa Guy Ryder, da babban sakataren hukumar hadin gwiwar raya tattalin arziki da ci gaba Angel Gurria, da kuma shugaban hukumar gudanarwar cibiyar daidaita hada hadar kudade Randal Quarles.

Mr. Li ya bayyana burin ganin an cimma daidaito, da karfafa gwiwa, da zurfafa hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, duka dai domin tabbatar da yanayi mai kyau na ci gaban tattalin arzikin duniya.

Taron dai shi ne karo na 4 tsakanin firaminista Li da wadannan jagororin cibiyoyin kudi 6. A bana taken taron shi ne "yayata bude kofa, daidaito da samar da managarcin ci gaban tattalin arzikin duniya".(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China