Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin zai tattauna da shugabannin hukumomin tattalin arziki na kasa da kasa
2019-11-15 19:38:22        cri
Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Jumma'a cewa, firaministan kasar Sin Li Keqiang, zai tattauna da shugabannin hukumomin tattalin arziki da harkokin kudi na kasa da kasa a ranar 21 ga watan Nuwanba a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugabannin sun hada da na bankin duniya David Malpass, da babbar darektan asusun ba da lamuni na duniya Kristalina Georgieva, da mataimakin babban darektan kungiyar cinikayya ta duniya Alan Wolff, da babban darektan hukumar kwadago ta duniya Guy Ryder, da sakatare janar na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki da raya kasa Angel Gurria da shugaban hukumar daidaita harkokin kudi Randal Quarles.

Abubuwan da ake saran za su tattauna sun hada da, yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki, manufofin gwamnati kan tsarin tattalin arziki, da yayata ci gaba tattalin arzikin kasar Sin ta yadda za ta kara bude kofa da yiwa tsarin tafiyar da tattalin arziki gyaran fuska.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China