Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya yi kira da daukar matakan kyautata dangantakar Sin da Japan
2019-11-04 20:04:04        cri

Firaministan Sin Li Keqiang, ya yi kira da a dauki matakan kara kyautata dangantakar Sin da Japan, da maida hankali ga cimma muradun bai daya na kasashen biyu, a kuma shawo kan batutuwa masu sarkakiya tsakanin su, da tabbatar da amincewa da juna, da wanzar da dangantakarsu yadda ya kamata.

Li ya bayyana hakan ne a yau Litinin a birnin Bangkok, yayin zantawar sa da firaministan Japan Shinzo Abe, a gefen taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin kan gabashin Asiya.

A nasa bangaren Abe, ya ce Japan na da aniyar karfafa tattaunawa, da gudanar da shawarwari tsakaninta da Sin, tana kuma burin zurfafa hadin gwiwar kai tsaye, tare da aiki tare da Sin a al'amura da suka shafi yankin su, da ma na kasa da kasa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China