2019-07-09 14:48:28 cri |
A safiyar ranar 9 ga wata, aka kammala taron zaman lafiya tsakanin sassa daban daban na kasar Afghanistan, a birnin Doha na kasar Qatar, wanda kasashen Qatar da Jamus suka shirya tare. A cikin sanarwar taron, an yi kirar yin shawarwari kan batun na Afghanistan daga dukkan fannoni.
Taron dai da aka bude a ranar 7 ga wata, ya samu halartar gwamnatin Afghanistan, kungiyar Taliban da rukunoni da dama na kasar. An mayar da wannan taro matsayin muhimmin ci gaba da aka samu wajen aikin shimfida zaman lafiya a Afghanistan. Da ma kungiyar Taliban ta mayar da gwamnatin kasar kamar 'yar tsana a hannun gwamnatin kasar Amurka, inda ta ki tattauna da ita kai tsaye. Ta yi shawarwari da gwamnatin Amurka kan aikin shimfida zaman lafiya a Afghanistan. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China