Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban hukumar bada agajin jin kai ta MDD ya tafi Sudan
2019-11-22 10:58:40        cri
Shugaban hukumar bada agajin jin kai na MDD Mark Lowcock, ya tafi Sudan, inda sama da mutane miliyan 8.5 ke bukatar taimako, biyo bayan matsalar tattalin arziki da barkewar cututtuka.

Mark Lowcock, mataimakin sakatare Janar na MDD kan ayyukan jin kai, zai shafe kwanaki 3 a kasar, daga ranar 22 zuwa 24 ga wata a ziyarar da ta zama ta farko da zai kai kasar tun bayan da aka kafa gwamnatin rikon kwarya a watan Augusta.

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce Mark Lowcock zai gana da jami'an gwamnatin Sudan da ma'aikatan jin kai.

Kakakin ya ce jami'in zai kuma je yankin Kassala dake gabashin kasar, domin ziyartar cibiyoyin lafiya da mutanen da matsarar tattalin arziki da barkewar cututtuka ya shafa da kuma matasa masu bada gudunmuwa wajen tunkarar yanayin da ake ciki.

Barkewar cututtuka da sauyawar yanayi da matsalar tattalin arziki, sun jefa mutane sama da miliyan 8.5, adadin da ake sa ran zai karu, cikin bukatar agaji. Daga ciki, akwai kusan mutane miliyan 2 da suka rasa matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China