Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta Kudu ta dage lokacin tattaunawar zaman lafiya ta kasar Sudan zuwa Disamba
2019-11-20 10:15:12        cri
Wani jami'in Sudan ta Kudu ya sanar a jiya cewa za'a maido da tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangaren gwamantin rikon kwaryar kasar Sudan da kungiyoyi 'yan adawa a watan Disamba a Juba sakamakon wasu dalilai da suka shafi tsare tsaren tattaunawar.

Tut Kew Gatluak, shugaban tawagar masu shiga tsakani na Sudan ta Kudu ya fadawa 'yan jaridu cewa, sabon zagayen tattaunawar wanda aka fara a ranar 14 ga watan Oktoba a Juba ana sa ran dawowa kan tattaunawar a ranar 21 ga watan Nuwamba, amma an dage zuwa ranar 10 ga watan Disamba kasancewa mambobi da dama na kungiyoyin 'yan tawaye suna cigaba da tattaunawar cimma daidaito da majalisar mulkin kasar Sudan, suna halartar wasu tarukan karawa juna sani a shiyyar wanda kungiyar tarayyar Afrika ta shirya.

Gatluak ya ce, Juba ta kasance wajen da za'a gudanar da tattaunawar. Kungiyoyin 'yan adawa suna cigaba da halartar tarukan karawa juna sani a wurare daban daban. Wasu kuma suna gudanar da tarukan a Addis Ababa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China