Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD tace an samu cigaba ta fannin magance cutar HIV/Aids
2019-11-27 09:49:45        cri

Wani sabon rahoton da shirin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki na MDD wato (UNAIDS) ya fitar a Kenya a jiya Talata ya tabbatar da cewa, an samu gagarumin cigaba wajen magance cutar mai karya garkuwa jiki wato HIV/AIDS a duk fadin duniya.

Rahoton ya nuna cewa ya zuwa tsakiyar shekarar 2019, an yi kiyasin kimanin mutane miliyan 24.5 daga cikin adadin mutane miliyan 37.9 dake dauke da kwayar cutar suna samun damar shan mugungunan cutar. Sakamakon yadda ake cigaba da karbar magungunan cutar, mutane kalilan ne suke mutuwa a sanadiyyar rashin lafiya mai nasaba da cutar ta AIDS," inji rahoton wanda aka gabatar a Nairobi.

Duk da irin cigaban da aka samu, rashin adalci a yayin zamantakewa, da rashin daidaito, da nuna tsangwama, suna kara haifar da koma baya ga shirin yaki da cutar HIV da ma shirin samar da dawwamamman cigaba na MDD. Winnie Byanyima, babbar daraktar shirin UNAIDS ita ce ta bayyana hakan a lokacin kaddamar da rahoton.

Rahoton ya ce, mata matasa da yara mata har yanzu suna fuskantar matsalolin kamuwa da sabbin kwayoyin cutar ta HIV, hudu daga cikin biyar na sabbin matasan da suke kamuwa da cutar a yankin Saharar Afrika mata ne.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China