Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bikin cika shekaru 10 da kafuwar yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Nijeriya da Guangdong
2019-11-28 14:03:07        cri


A ranar 26 ga wata, an gudanar da bikin taya murnar cika shekaru 10, da kafuwar yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Nijeriya da lardin Guangdong na kasar Sin. Cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, an kafa kamfanonin kere-kere dake kan gaba cikin Nijeriya, har ma cikin dukkanin yammacin kasashen Afirka a wannan fanni, lamarin da ya zama muhimmiyar alama ta hadin gwiwar Sin da Nijeriya ta fuskar harkokin masana'antu.

Bisa labarin da aka samu, an ce, a wannan rana, wakilin mataimakin shugaban kasar Nijeriya, kana ministan harkokin masana'antu, cinikayya da zuba jari Otunba Richard Adeniyi Adebayo, da wasu jami'an gwamnatin jihar Ogun, da karamin jakadan Sin dake birnin Lagos Chu Maoming, da mashawarci jakadan Sin kan harkokin kasuwanci dake kasar Nijeirya Li Yuan, da mataimakin shugaban kamfanin New South na lardin Guangdong na kasar Sin Deng Yu da dai sauransu sun halarci bikin.

Yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Nijeriya da Guangdong yana jihar Ogun dake kudu maso yammacin Nijeriya, wanda yake da kusanci da cibiyar tattalin arzikin kasar, wato jihar Lagos, kuma an bude yankin ne a watan Mayu na shekarar 2009. Daga watan Yuli na shekarar 2016, kamfanin New South na lardin Guangdong ya dauki nauyin gudanar da harkokin wannan yanki. Mataimakin shugaban kamfanin New South, kana babban manajan kamfanin zuba jari a kasashen ketare Deng Yu ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, gaba daya akwai kamfanoni 63 da suka yi rajista a yankin, wadanda suka hada da masana'antun samar da kayayyaki na amfanin yau da kullum, da kayayyakin cikin gida, da kayayyakin karfe, da kayayyakin gine-gine da katako da sauransu, kuma ana bunkasa harkokin sarrafa katako, gine-gine, da cinikayya cikin hadin gwiwa a wannan yanki, lamarin da ya samar da guraben ayyukan yi sama da dubu 6 ga mazauna wurin.

Da yake tsokaci kan halin da wannan yanki yake ciki, Deng Yu ya bayyana cewa, "A da, akwai wahalar samun jari, amma yanzu, akwai kamfanoni da dama da suke neman shiga yankin, har ma wasu suna zuwa da cikakken daftari. Kuma ba kamar a da ba, a lokacin da ba wanda ke son yin hadin gwiwa da sauran kamfanoni, yanzu, akwai kamfanoni da mambobin kungiyar kasuwanci da dama dake yin hadin gwiwa, muna samun karin kamfanoni a yankin. Ina ganin cewa, muna cikin lokaci na musamman na neman bunkasuwa."

Wakilin mataimakin shugaban kasar Nijeriya, kana ministan masana'antu, cinikayya da zuba jari na kasar Otunba Richard Adeniyi Adebayo ya nuna yabo matuka, kan sakamakon da yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya samu cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, ya ce, yankin na ba da muhimmin taimako ga kasar wajen kyautata hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Nijeirya, da ma inganta harkokin masana'antu cikin kasar Nijeriya. Yana mai cewa, "Yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na Nijeriya da Guangdong, ya ba da taimako ga Nijeriya wajen raya harkokin masana'antunta, inda karfin kayayyakin da yankin yake samarwa a ko wace shekara ya kai dallar Amurka miliyan 234, kuma gaba daya an zuba jarin sama da dallar Amurka miliyan dubu 2, inda aka kuma baiwa mazauna sama da dubu 6 guraban aikin yi. Lamarin da ya ba da tabbaci ga samun dauwamammen ci gaba ta fuskar harkokin masana'antu a Nijeriya, da kuma kara karfin yankin wajen raya tattalin arziki."

Kamfanin gilashi na kasar Sin, shi ne kamfanin Sin mafi girma da aka kafa cikin yankin, fadin gidajen kamfanin ya kai muraba'in mita dubu 250. A ranar 18 ga watan Oktoba na bana, an bude na'urar samar da gilashi irin na Float, wadanda za su iya samar da gilashi ton 500 cikin ko wace rana. Ma'anar ita ce, za a sami gilashi na amfanin gine-gine masu inganci cikin gajeran lokaci mai zuwa. Babban manajan kamfanin Cui Baoyu ya bayyana cewa, "A ko wace shekara, za mu iya samar da gilashi ton dubu 250, kuma wannan shi ne mataki na farko. A nan gaba kuma, za mu ci gaba da sarrafa gilashin Float. Ko shakka babu, jarin da kamfaninmu ya zuba a nan kasar Nijeriya, ya ba da gudummawa wajen raya tattalin arzikin kasar baki daya, domin bisa kididdigar da muka yi, sana'ar ta samar da gilashi na iya raya sauran sana'o'i guda 15 a kasar, kamar su hakar ma'adinai, da zirga-zirga, da harkokin tashoshin jiragen ruwa da dai sauransu. Cikin mataki na farko, mun samar da guraben aikin yi ga mazauna wurin kimanin dari uku zuwa dari hudu."

Yayin bikin na wannan rana, an kuma kulla yarjejeniyar shiga yankin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na Nijeriya da Guangdong, da ma wasu sabbin kamfanoni, da wasu takardu na fahimtar juna. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China