Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Annobar zazzabin shawara ta kashe mutane 24 a arewa maso yammacin Najeriya
2019-10-31 10:25:21        cri
Jami'an lafiya a Najeriya sun sanar a jiya Laraba cewa annobar cutar zazzabin yellow fever, ko shawara, ta yi sanadiyyar rayuka 24 a jahar Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Kabir Mustapha, babban sakataren ma'aikatar lafiyar jahar Katsina yace, domin daukar matakan rigakafin cutar, gwamnatin jahar ta samar da alluran riga kafi kimanin miliyan 7, kawo yanzu, an riga an yiwa mutane miliyan 6.3 alluran riga kafin cutar tsakanin 'yan watanni 9 zuwa shekaru 44 da haihuwa.

Babu wani magani takamaimai na warkar da cutar, duk da kasancewar ana iya yin rigakafin kamuwa da cutar ta hanyar amfani da alluran rigakafin cutar zazzabin ta yellow fever, inda zasu samar da garkuwa ga jikin dan adam.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China