Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ya tagayyara al'ummomin yankuna 60 a tsakiyar Najeriya
2019-11-16 16:31:48        cri
A kalla al'ummomin yankuna 60 ne ambaliyar ruwa ta yi wa mummunar barna a jahar Nasarawa, dake shiyyar tsakiyar Najeriya, wani jami'in hukumar bada agajin gaggawa na yankin ne ya bayyana hakan a jiya Juma'a.

Jahohin dake shiyyar tsakiyar Najeriya sun sha fuskantar mummunar ambaliyar ruwa tun daga watan Augasta, sakamakon mamakon ruwan sama da aka sheka, gami da iska mai karfi, da kuma tumbatsar koguna da tafkuna.

Allu Maga, shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar Nasarawa ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dubban mutane ne suka kauracewa muhallansu da kuma hasarar dukiya ta miliyoyin nairori.

A cewar jami'in, al'ummomin da lamarin ya shafa sun hada da mutanen dake zaune a gabar tekun Benue. Ya kara da cewa, tun da farko an yi wa al'ummomin dake zaune a wadannan yankunan gargadin yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa amma suka yi biris tare da yin ikirarin cewa filayen dake yankunan sun gada ne daga iyaye da kakaninsu.

Maga yace, tuni gwamnatin jahar ta fara rabon kayayyakin tallafi ga mutanen da iftila'in ya shafa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China