Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kira jami'in ofishin jakadancin Amurka don gabatar da korafi game da dokar da ta shafi yankin HK
2019-11-20 19:57:55        cri

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu, ya gayyaci mukaddashin babban jami'in ofishin jakadancin Amurka dake kasar Sin William Klein, domin gabatar masa da korafin Sin, game da kudurin da majalissar dattijan Amurka ta gabatar, game da hakkin bil Adama da dimokaradiyya a yankin Hong Kong na Sin.

Ma Zhaoxu ya ce, Sin na fatan Amurka za ta dauki matakan gaggawa na dakatar da kudurin daga zama doka, ta kuma dakatar da tsoma baki nan take cikin harkokin Hong Kong, da ma sauran batutuwa da suka jibanci cikin gidan Sin. Ya ce idan har Amurka ta ki aiwatar da hakan, a nata bangaren Sin za ta aiwatar da martani, wanda ko shakka babu ba zai yiwa Amurkar daidi ba.

Jami'in na Sin ya kara da cewa, majalissar dattijan Amurka ta yi kutse cikin harkokin yankin Hong Kong, da harkokin cikin gidan Sin, matakin da ya yi matukar sabawa dokokin kasa da kasa, da ma tsare tsaren gudanar da huldar kasashen duniya, matakin da sam, Sin ba za ta taba lamunta ba.

Ma ya kuma jaddada cewa, gwamnatin Sin ta himmatu, wajen kare 'yancin mulkin kai, da tsaro da ci gaba, da ma muradun kasar ta. Za kuma ta ci gaba da aiwatar da manufar nan ta kasa daya tsarin mulki biyu, ba kuma za ta lamunci duk wani mataki na tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong ba. Daga nan sai ce Sin na jan kunnen Amurka, da ta sani cewa, duk wani yunkuri na gurgunta ci gaba da daidaiton yankin Hong Kong, ko kawo cikas ga ci gaban Sin, mummunan sakamakon sa zai koma ne ga Amurka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China