Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta sanya takunkumi kan kamfanonin Amurka dake da hannu a sayarwa yankin Taiwan makamai
2019-07-12 20:37:29        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang, ya bayyanawa taron manema labarai Jumma'ar nan cewa, kasarsa za ta sanya takunkumi kan kamfanonin Amurka dake da hannu wajen sayarwa yankin Taiwan makamai.

Kalaman Geng na zuwa ne, bayan da a baya Amurka ta bayyana shirinta na sayarwa yankin na Taiwan makamai da darajarsu ta kai dala biliyan 2.22. Ya ce, sayarwa yankin na Taiwan makamai da Amurka za ta yi, ya keta dokokin kasa da kasa, da tushen alakar kasashen biyu da manufar kasar Sin daya tak a duniya da ma sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da aka gabatar tsakanin sassan biyu. Haka kuma matakin ya saba 'yanci da tsaron kasar Sin. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China