Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNECA ta bukaci kasashen Afirka su aiwatar da tsare tsaren da zasu bunkasa yarjejeniyar AfCFTA
2019-06-13 14:13:00        cri
Hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD (ECA) ta bukaci kasashen Afrika dasu tsara wani shirin da zai taimaka wajen cikakkiyar aiwatarwa don cin moriyar yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci ta kasashen Afrika wato (AfCFTA).

ECA ta bayyana cikin wata sanarwa cewa yana da muhimmanci ga mambobin kasashen Afrika dake cikin kungiyar tarayyar Afrika (AU) su shirya dabarun aiwatar da yarjejeniyar cinikin wanda ya dace da moriyar kowace kasa dake nahiyar.

Haka zalika ECA tace a shirye take ta tallafawa kasashen Afrikan wajen bunkasa cigabansu karkashin dabarun dake kunshe cikin yarjejeniyar ta AfCFTA.

Hukumar ECA tayi wannan kiran ne makonni kadan bayan da yarjejeniyar kafa tsarin ciniki marar shinge tsakanin kasashen nahiyar wato (AfCFTA) ya fara aiki daga ranar 30 ga watan Mayu, inda kawo yanzu mambobin kasashen AU 22 suka amince da yarjejeniyar.

AfCFTA ta aza wani tubali na yin cinikayya marar shinge wanda shine mafi girma a duniya inda kasashen suka amince su shiga tsarin, wanda ya hade mutane sama da biliyan 1.2, kuma ya shafi karfin tattalin arzikin GDP na dala triliyan 2.5, in ji kungiyar AU.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China