Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in hukumar ECA ya ce kafa yankin ciniki maras shinge zai bunkasa tattalin arzikin Afrika
2019-06-02 14:46:29        cri

Babbar sakatariyar hukumar raya tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), Vera Songwe, ta ce yarjejeniyar kafa yankin ciniki maras shinge ta Afrika (AfCFTA), wadda ta fara aiki a ranar Alhamis da ta gabata, za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar ta Afrika.

Songwe ta bayyana hakan a lokacin wata ganawa da shugaban kwamitin raya tattalin arzikin Turai, Luca Jahier, da yammacin Juma'a, kamar yadda hukumar ECA ta bayyana.

A yayin da yarjejeniyar ta AfCFTA ta fara aiki a ranar Alhamis, kasashen Afrika karkashin kungiyar tarayyar Afrika (AU) za su kaddamar da fara aiwatar da shirin yarjejeniyar a watan Yulin wannan shekara a lokacin taron koli na AU da za'a gudanar a birnin Niamey, na Jamhuriyar Nijer.

Songwe, a lokacin ganawarta da wakilin na EU, ta bayyana irin rawar da yarjejeniyar ta AfCFTA za ta taka a matsayin wani ginshikin bunkasa cigaban tattalin arzikin Afrika, da bunkasa kayayyakin more rayuwa, da kuma taimakawa wajen magance matsalolin tattalin arziki wanda ke yin sanadiyyar kwararar 'yan ci rani daga nahiyar zuwa kasashen Turai, kamar yadda ECA ta sanar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China