Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya yi kira da a kafa kotunan musamman don inganta tsarin shari'a
2019-11-26 20:31:33        cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga jami'an shari'a da su yi kokarin kafa kotuna na musamman, don hanzarta tafiyar da harkokin mulki da ma yanke hukunci a kasar.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne, yayin bude taron shekara-shekara na alkalan manyan kotunan kasar na shekarar 2019 da ya gudana a Abuja, fadar mulkin kasar. Yana mai cewa, kafa managarcin tsari ga kotunan kula da manyan laifuffuka na musamman ko mayar da kotunan da ake da su a matsayin kotunan musamman tare da samar musu jami'an shari'a da suka cancanta, zai taimaka wajen kawar da tarnakin harkokin mulki da ake fuskanta wajen yanke hukunci.

Ya ce, gwamnati ta himmantu wajen farfado da tattalin arzikin kasar, musamman ta hanyar janyo hankulan masu sha'awar zuba jari daga ketare da ma yaki da matsalar cin hanci da tsaro. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China