2019-11-24 16:34:33 cri |
A ranar 23 ga watan Nuwamban da muke ciki, an kaddamar da kungiyar daidaita da ciyar da aikin samar da kaya gaba ta kamfanonin kasar Sin dake kasar Najeriya, a birnin Abuja, hedkwatar Tarayyar Najeriya, inda a wajen bikin kaddamarwa, minista Zhao Yong dake ofishin jakadancin kasar Sin a Najeriya, ya yanke kyalle don bude kungiyar.
Wannan kungiya an samu damar kafa ta ne bisa goyon bayan da ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Najeriya ya nuna. Daga bisani an yi rajistar wannan kungiyar al'ummun kasar Sin a Najeriya, wadda ta kunshi mambobi kamfanonin jarin kasar Sin 21. Dukkansu kamfanoni ne masu zaman kansu na kasar Sin, wadanda ke zuba jari da gudanar da harkoki a kasar Najeriya. Sa'an nan makasudin kungiyar shi ne: Gadon al'adun gargajiya masu alaka da hanyar cinikin siliki ta kasar Sin, da yada ruhu na 'yan kasuwa Sinawa, da neman hada kan Sinawa, da zama dandalin sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Najeriya, gami da ciyar da harkokinsu gaba.
Kamfanin ZOCEC shi ne ya jagoranci kungiyar kamfanonin kasar Sin a wannan karo, yayin da kamfanonin Uni-President da Lee Group su ma suka samu matsayin shugabanci mai daraja. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China