Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutanen da suka gujewa muhallansu 100,000 ne ambaliyar ruwa ta yiwa tarko a arewa maso gabashin Najeriya
2019-11-14 10:00:15        cri
Kimanin mutanen dake rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira 100,000 a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ambaliyar ruwa ta yiwa kawanya a wani garin dake kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Kamaru, wata jami'ar yankin ta bayyana hakan a ranar Laraba.

Sama da hekta 4,000 na gonaki ne ambaliyar ruwan ta lalata a garin Rann, dake karamar hukumar Kalabalge na jihar Borno, a cewar Zainab Gimba, 'yar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar yankin.

Gimba ta ce kogin Kaalia dake Kamaru ne ya tumbatsa inda ya haddasa barnar.

A cewar Gimba, daga cikin mutanen da lamarin ya fi shafa akwai dubban mata da kananan yara wadanda ambaliyar ruwan ta danawa tarko na rashin samun abinci, muhalli, da kayayyakin more rayuwa.

Mutanen suna bukatar dauki don kwashe su daga wajen, kasancewar ragowar sansanonin 'yan gudun hijirar dake kusa da su su ma suna fuskantar kalubaloli da suka hada da cunkuson jama'a ko kuma yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwan, Gimba ta tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho.

Ta bukaci a kai daukin gaggawa don dakile matsalar ambaliyar ruwan, da kuma taimakawa mutanen da lamarin ya shafa, ta ce, gaza daukar matakan da suka dace zai iya sanadiyyar salwantar rayuka masu yawa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China