2019-11-20 09:14:15 cri |
A jawabin da ya gabatar a wajen bude taron kolin wuni biyu game da matakan dakile ayyukan rashawa a ma'aikatun gwamnati, shugaba Buhari ya ce, tilas ne dukkan sassan ma'aikatu da hukumomin gwamnatin su hada hannu wajen yakar rashawa kuma su aiwatar da wadannan matakai na yaki da rashawar yadda ya kamata.
A cewar shugaban na Najeriya, rashawa shi ne tushen dukkan matsalolin da suka dabaibaye kasar mafi yawan al'umma ta yammacin Afrika, wanda ya haifar da talauci, tabarbarewar tsaro, durkushewar ilmi, rashin ingancin kayayyakin kiwon lafiya, da ayyukan hidima, da haddasa dunbun matsalolin ga yanayin zaman rayuwar al'umma.
Shugaban ya ce, gwamnatinsa tana aiki tukuru domin kawo karshen wadannan illoli. Matsalar rashawa musamman a fannonin hukumomin gwamnati, su ne suke haifar da koma baya ga yunkurin gwamnatoci wajen samar da muhimman kayayyakin more rayuwa ga al'ummar kasar.
Shugaban Najeriyar ya bayyana rashawa a matsayin babbar barazana dake kawo cikas wajen cimma nasarar shirin samar da dawwamaman cigaba na MDD, da shirin sauye sauyen bunkasa tattalin arzikin kasar, wanda a cewar shugaba Buhari gwamnatinsa tana yin aiki tukuru domin bunkasa cigaban kasar. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China