2019-11-19 09:38:27 cri |
A cewar sanarwar, an kwashi bakin hauren ne daga filin jirgin saman kasa da kasa na Benina Benghazi zuwa birnin Legas dake Najeriya.
A ranar Lahadi, sashen kula da bakin hauren ya tisa keyar wasu bakin hauren sama da guda 60 daga Benghazi zuwa Chad da Sudan.
Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa ta ce, a 'yan kwanakin nan cibiyoyin kasar Libya suna tsare da bakin haure sama 650,000, daga cikin adadin akwai mata da kananan yara kimanin 6,000.
Bakin hauren wadanda galibinsu 'yan kasashen Afrika ne, wadanda ke neman tsallaka tekun Mediterranean daga kasar Libya zuwa kasashen Turai a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalolin tabarbarewar tsaro da tashe tashen hankula tun bayan kifar da gwamnatin marigayi tsahon shugaban Libya Muammar Gaddafi a shekarar 2011. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China