Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya bukaci Sin da ASEAN su martaba tsarin kasancewar bangarori daban-daban
2019-11-04 10:45:12        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bukaci kasarsa da kungiyar ASEAN da su ci gaba da martaba tsarin kasancewar bangarori daban-daban da yin cikikayya cikin 'yanci, da jurewa hadurra da samun ci gaba na bai daya.

Li ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron shugabannin Sin da kungiyar ASEAN karo na 22 da ya gudana a Bangkok na kasar Thailand. Ya ce, tun lokacin da sassan biyu suka kulla alakar tattauna a tsakaninsu, sun samar da moriya ga juna da ma shiyyar baki daya. Yana mai cewa, kasar Sin tana goyon bayan ASEAN a matsayin jagorar alakar yankin gabashin Asiya.

Firaministan na kasar Sin ya ce, ya kamata kasar Sin da kasashen ASEAN, su nace ga akidar sakamakon nasara da cin moriya tare, da hanzarta aikin daga matsayin alakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.

Ya kuma yi kira da a hanzarta kammala yarjejeniyar da aka cimma, kan alakar tattalin arziki na shiyyar (RCEP), ta yadda za a aza harsashin dunkulewar tattalin arzikin gabashin Asiya, da aiwatar da yarjejeniyar yankin cinikayya cikin 'yanci na Sin da ASEAN da aka daga matsayinta, da nufin bunkasa harkokin cinikayya da saukaka zuba jari.

Li ya jaddada cewa, kasar Sin za ta nace ga turbar samun bunkasa cikin lumana da aiwatar da manufar bude kofa da zai amfanawa kowa. Ya ce, a shirye kasar Sin take ta hade shawarar ziri daya da hanya daya da dabarun raya kasa na ASEAN da ma mambobinta baki daya (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China