Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun Amurka da za a janye daga Syria za su koma yammacin Iraqi
2019-10-21 10:19:08        cri
Sakataren tsaron Amurka, Mark Esper, ya ce dakarun kasar kimanin 1,000 da za a janye daga arewa maso gabashin Syria, za su koma yammacin Iraqi, domin taimakawa wajen kare kasar da yaki ya daidaita, da kuma aikin yakar kungiyar IS.

Sanarwar da hukumar tsaron kasar ta fitar jiya, ta ruwaito Mark Esper wanda a lokacin ke kan hanyarsa ta zuwa Afghanistan na cewa, ana ci gaba da janye dakarun Amurka cikin sauri, kuma za a dauki makonni ba raneku ba. Yana mai cewa suna son gudanar da aikin cikin amince da taka tsantsa.

Amurka na ta janye sojojinta kusan 1,000 daga arewacin Syria, yayin da dakarun Turkiyya ke tsaka da kai har-hare kan mayakan Kurdawa a sassa daban-daban na arewa maso gabashin Syria da aka kaddamar makonni biyu da suka gabata.

A makon da ya gabata ne, shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da cewa dakarun Amurka za su bar Syria, amma kuma za su ci gaba da kasancewa a yankin gabas ta tsakiya domin bibiyar yanayin yankin, yayin da wani adadi kalilan na dakarun za su zauna a sansanin sojin na At Tanf dake kudancin Syria domin yaki da ragowar kungiyar IS. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China