Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka da ta daina tsoma baki cikin harkokin yankin HK
2019-11-19 19:26:47        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ja hankalin Amurka da ta kauracewa tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong. Kalaman na Geng Shuang, na zuwa ne bayan da aka jiyo sakataren wajen Amurka Mike Pompeo, yana cewa kasar sa ta damu matuka, da karuwar tashe tashen hankula a Hong Kong, yana mai kira ga mahukuntan yankin da su dauki matakin sauke nauyin jagoranci dake wuyan su, domin kawo karshen fadace fadace.

Game da hakan, Mr. Geng ya ce tashe tashen hankula dake aukuwa a Hong Kong na jefa rayuwar al'umma cikin hadari, suna karya doka da oda, tare da yin karan tsaye ga akidar nan ta kasa daya tsarin mulki biyu, tare da jefa yankin baki daya cikin wani mawuyacin hali.

Ya ce muhimmin aiki dake gaban komai a yanzu, shi ne dakatar da tashe tashen hankula, kuma gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, na goyon bayan jagorar yankin Hong Kong, da gwamnatin yankin, da 'yan sanda da kuma sashen shari'a.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China