Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu ba da taimako 3 na kungiyar IOM sun rasu a Sudan ta kudu
2019-10-31 11:03:56        cri
Jami'in reshen Sudan ta kudu na kungiya mai kula da harkokin makaurata ta kasa da kasa Jean Philippe Chauzy ya bayyana a jiya Laraba cewa, an yi musanyar wuta a garin Morobo dake kan iyakar kasa a kudu a ran 27 ga wata, inda masu aikin sa kai na kungiyar dake gudanar da aikin ringakafin cutar Ebola a wurin sun rasu, yayin da wasu 2 suka ji rauni.

Ban da wannan kuma, masu fafutuka sun yi garkuwa da dan wani mamaciya mai aikin sa kai mai shekaru 4 da haifuwa, da wata mace mai aikin sa kai, ba a jin duriyarsu ba tukuna. Kungiyar ta riga ta dakatar da aikin da take gudana a tasoshin sa ido kan cutar Ebola 5 dake kan iyakar dake tsakanin Kongo Kinshasa da Sudan ta kudu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China