Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Afirka ta Kudu
2019-11-15 11:00:27        cri

Jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa a birnin Brasilia, fadar mulkin kasar Brazil.

A yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya ce, kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu su ne manyan kasashe masu tasowa da kuma kasashe masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, inda ya ce suna da nauyin raya tattalin arziki da kuma kyautata zaman rayuwar al'umma a cikin gida, yayin da a waje kuma, suke tsayawa tsayin daka wajen kiyaye harkokin cinikin tsakanin kasa da kasa, da kuma nuna adawa da kariyar ciniki. Ya ce Kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwa da kasar Afirka ta Kudu, domin kiyaye hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare.

A nasa bangare kuma, Matamela Cyril Ramaphosa ya taya kasar Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwar kasar Sin, inda ya ce, kasarsa tana yabawa matuka kan manyan sakamakon da jama'ar kasar Sin suka cimma bisa jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar, kuma tana goyon bayan kasar Sin wajen neman ci gaba. A sa'I daya kuma, ya ce, kasar Afirka ta Kudu ba ta yarda da wasu kasashen duniya kan harkokin rashin adalci da suka yi wa kasar Sin ba, kuma tana goyon bayan kasar Sin wajen kiyaye ikonta yadda ya kamata.

Bugu da kari, ya yi bayani kan ayyukan da kasar Afirka ta Kudu za ta yi a lokacin da za ta shugabanci kungiyar tarayyar kasashen Afirka a shekara mai zuwa. Inda ya ce, kasar Afirka ta Kudu tana sa ran karfafa dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da ba da taimako ga kasashen Afirka wajen shimfida zaman lafiya da zaman karko, ta yadda za su iya fara kwaskwarima kan harkokin masana'antu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China