Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin ya bukaci kasashen duniya da su taimakawa Somaliya ta inganta tsarin shugabancinta
2019-11-22 10:36:14        cri

Mataimakin wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga al'ummomin kasashen duniya, da su taimakawa kasar Somaliya ta yadda za ta inganta tsarinta na shugabanci.

Wu Haitao ya yi wannan kira ne, yayin zaman kwamitin sulhun MDD kan yanayin da ake ciki a kasar ta Somaliya, yana mai cewa, ya kamata kasa da kasa, su ci gaba da mayar da hankali kan halin da ake ciki a kasar da ma sassan da kasar ke bukatar taimako, ciki har da "taimakawa Somaliyar ta inganta tsarinta na shugabanci da kara karfinta na tsaro gami da goyon baya".

Wakilin na kasar Sin, ya ce, ya kamata kwamitin sulhu gami da al'ummomin kasa da kasa, su martaba tsarin jagoranci da 'yancin kasar ta Somaliya, hakan zai taimakawa kasar inganta tsarinta na siyasa, da kara karfin hukumomin tarayya da inganta alaka tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohin kasar, ta yadda za a samar da yanayin da ya dace na gudanar da zabukan shekara mai zuwa lami lafiya ba tare da wata matsala ba, da kara karfin matakan tsaron da kasar take dauka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China