![]() |
|
2019-07-13 16:16:34 cri |
Kakakin ya kara da cewa, Guterres, ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, kana ya yi fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
Tun da farko a ranar Juma'a, wasu 'yan bindiga masu dauke da makamai suka nufi otel din dake tashar ruwan birnin Kismayo a kasar Somaliya, inda suka jibge motoci makare da ababen fashewa a mashigar otel din.
Shi dai wannan otel, ya shahara sosai a matsayin wajen zaman mambobin majalisar dokokin da ministocin kasar. An ba da rahoton cewa, wasu daga cikin 'yan majalisun dokokin kasar suna zaune a cikin otel din a lokacin kaddamar da harin.
A daidai wannan lokaci otel din ya karbi bakuncin wasu wakilan shirya zabukan shugaban kasa da na majalisun dokoki a Jubaland, yanki mai cin gashin kansa dake kudancin Somaliya. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China