Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 9 sun mutu, wasu 6 kuma sun jikkata yayin wani rikici a kudancin Somalia
2019-09-16 10:33:52        cri
Mutane 9 sun mutu, yayin da wasu 6 suka jikkata yayin wata arangama tsakanin dakarun gwamnati da mayakan al-Shabab, da yammacin ranar Asabar, a garin Qoryoley dake yankin Lower Shabelle na kasar Somalia.

Gwamnan Qoryoley, Said Ali Ibrahim, ya ce mayakan sun kai hari kan garin har sau 2, amma dakarun suka dakile yunkurinsu. Ya ce harin ya rutsa da wasu mazauna yankin, inda mutane 9 suka mutu yayin da wasu 6 suka jikkata.

Ya ce yanzu dakarun gwamnati na rike da iko da garin, inda suka hana mayakan kwace shi.

Wani mazauni yankin Lul Elmi, ya shaidawa Xinhua ta wayar tarho cewa, mayakan Al Shabaab ne suka fara kai hari kan dakarun, inda dakarun na wanzar da zaman lafiya na tarayyar Afrika, suka mayar da martani ta hanyar harba makaman roka zuwa wuraren da mayakan suke, yana mai cewa mutane da dama sun mutu yayin da wasu suka jikkata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China