Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun Somaliya sun hallaka mayakan Al-Shabab 9
2019-09-02 20:37:03        cri
A Litinin din nan ne dakarun sojojin kasar Somaliya, suka sanar da hallaka mayakan 'yan ta'adda na Al-Shabab su 9, yayin wani hari da suka kai maboyar kungiyar dake kudancin kasar a jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da hakan, kwamandan sashi na 35, na bataliya ta 7 Ali Abdullahi Araye, ya ce sojojin sun kai hari maboyar 'yan ta'addan ne bayan samun rahotannin sirri daga al'ummun kauyukan Kaxarey, da Busley da Baldof, wadanda suka shaidawa sojojin cewa mayakan na fake a yankunan su, har ma suna dora musu haraji.

Araye ya kara da cewa, bayan dauki ba dadi da mayakan, sojojin gwamnati sun ci galaba a kan su, inda suka hallaka 9, yayin da wasu da dama kuma suka tsere. Kaza lika sojojin sun kone ababen hawa da Babura da dama, wadanda 'yan ta'addan ke amfani da su wajen dakon ababen fashewa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China