![]() |
|
2019-09-23 10:36:15 cri |
Rundunar sojojin gwamnatin Somaliya, ta sanar da cewa, jiya dakarunta sun yi nasarar kashe 'yan ta'addan Al shabaab 13 a kudancin kasar.
Mai magana da yawun rundunar sojin ya shedawa manema labarai cewa, , 'yan ta'adda sun kai hari kan wani sansanin sojin gwamnati dake kudancin kasar a safiyar wannan rana, kuma nan da nan sojojin sun mayar da martani tare da dakile harin. Ya ce 'yan ta'adda 13 sun mutu a musanyar wutan da suka yi da sojojin gwamnati, yayin da wasu daga sojojin gwamnati suka ji rauni.
Kungiyar Al Shabaab ta yi ikirari cewa, ta kashe sojojin gwamnati 20 a farmaki da suka kai a wannan rana.
Rahotanni na cewa, kungiyar na da alaka da Qaeda, kuma sun sha kai hare-hare a Somaliya da sauran kasashe dake kewaye a 'yan shekarun nan. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China