Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AL da Masar sun yi Allah wadai da mummunan harin da aka kai a wani otel a Somaliya
2019-07-15 10:43:08        cri

Kungiyar kasashen Larabawa (AL) ta yi Allah wadai da mummunan harin ta'addanci na baya-bayan nan da aka kai ranar Asabar kan wani otel dake garin Kismayo mai tashar jiragen ruwa dake kasar Somaliya, harin da ya hallaka mutane a kalla 26 kana wasu 56 kuma suka jikkata

Ita ma kasar Masar cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta yi Allah wadai da harin.

Wani rahoto da MDD ta fitar a kwanakin baya na nuna cewa, daga watan Janairu 2016 zuwa watan Oktoban 2017, sama da mutane 2,000 ne suka mutu, kana sama da mutane 2,500 kuma suka jikkata, a tashin hankalin dake faruwa a kasar Somaliya, sakamakon hare-haren da mayakan Al-Shabaab ke kaddamarwa a sassan kasar. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China