Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jaridar The New York Times tana neman shafa wa jihar Xinjiang kashin kaza
2019-11-20 14:26:58        cri


Kwanan baya, jaridar The New York Times ta kasar Amurka ta wallafa wani rahoton da ke neman bata sunan shirin yaki da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da ake gudanarwa a jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Dangane da wannan batu, kakakin jihar Xinjiang ya bayyana cewa, bayanin da jaridar The New York Times ta wallafa karya ne, wanda abokan gaba na gwamnatin kasar Sin dake cikin gida da waje suka rubuta cikin hadin gwiwa domin neman bata sunan kasar.

Jaridar The New York Times ta kasar Amurka mai shekaru 160 ta mai da kanta kafar watsa labarai ta koli a yammacin duniya. Amma, babbar jaridar ta kan wallafa bayanan karya, lamarin da ya nuna rashin kwarewar wannan jarida. Tun daga shekarar 2003, a kan ga 'yan jaridu na jaridar The New York Times suna rubuta bayanai na karya, ko kuma su saci bayanan wasu mutane, lamarin da a baya har ya sa shugaban jaridar ta The New York Times yin murabus sabo da kunya.

Game da bayanan da jaridar ta fidda ta fuskar batutuwan kasar Sin kuma, ana iya cewa, duk wani abu da ya shafi kasar Sin, tabbas ne jaridar The New York Times za ta fadi laifinsa, musamman ma kan batutuwan dake shafar jihar Xinjiang ta kasar, don nuna adawa ga kasar Sin, tare da kuma da biyan bukatun 'yan siyasa na kasashen yamma da ke adawa da bunkasuwar kasar Sin.

Ko shakka babu, wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya, ciki hada da jaridar The New York Times suna adawa da kasar Sin, har ma ba su bayyana bunkasuwar kasar Sin a fannoni daban daban yadda ya kamata, nuna adawa da kasar Sin shi ne abin da suka fi mayar da hankali a kai. Kuma babban burinsu shi ne, taimaka wa 'yan siyasa na kasashensu wajen sa hannu cikin harkokin cikin gida na kasar Sin. Kamar yadda dan jaridar kasar Amurka Andre Vltchek ya ce, "Wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya na ganin cewa, duk abin da kasar Sin ta yi, laifi ne. Kana, babban laifin kasar Sin shi ne, tana ci gaba da bunkasuwa."

Amma, sanin kowa ne cewa, jihar Xinjiang ta samu babban ci gaba wajen yaki da masu tsattsauran ra'ayi da 'yan ta'adda cikin 'yan shekarun nan. Cikin shekaru 3 da suka gabata, ba a samu wani harin ta'addanci da aka kai a jihar Xinjiang ba, kuma ana kiyaye 'yancin al'ummomin jihar a fannonin tsaro, kiwon lafiya da neman ci gaba yadda ya kamata. Daga karshen shekarar da ta gabata, ya zuwa yanzu, akwai tawagogin kasashen ketare da dama da suka kai ziyara a jihar Xinjiang, inda suka bayyana yabo kan aikin yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi da ake gudanarwa a jihar Xinjiang na kasar Sin. Ciki hada da dan kasar Amurka Val Thomposn, bayan ziyararsa a jihar, ya rubuta wani sharhi a mujallar International Focus ta kasar Amurka, inda ya bayyana cewa, ana gudanar da harkoki yadda ya kamata a cibiyar koyar da sana'o'i dake yankin Kashgar yadda ya kamata, daliban cibiyar suna jin dadin zama da ma gudanar da harkokinsu na karatu, a ganinsa, dukkan dalibai suna farin ciki kwarai da gaske.

Haka kuma, wakilin kasar Belarus ya taba ba da jawabi a madadin kasashe guda 54, inda ya nuna goyon baya kan matakan da kasar Sin ta dauka wajen yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi. Ya kuma nuna adawa da yadda kasashen Amurka da Burtaniya suke fakewa da batun kare hakkin bil-Adama, suna tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin. Lamarin da ya nuna cewa, kasashen duniya suna iya bambance gaskiya da kuma karya game da batun hakkin dan Adam da ma ci gaba a jihar Xinjiang, abin da wasu kasashen yammaci suke yi, shi ne kawai neman bata ran al'ummomin duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China