Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bayyana ra'ayinta kan batun Xinjiang
2019-09-24 14:02:22        cri

Kakakin tawagar kasar Sin da ke halartar babban taron MDD karo na 74 ya kira taron manema labarai don bayyana ra'ayin kasarsa, kan taron da Amurka ta shirya kira game da kiyaye 'yancin bin addinai da batun da ya shafi jihar Xinjiang ta kasar Sin.

A jiya ne, Amurka ta kira taro mai taken "yin kira don a kiyaye 'yancin bin addinai" a babbar hedkwatar MDD, inda mataimakin shugaban kasar Mike Pence ya zargi kasashe da dama ciki har da kasar Sin kan yadda suke kare 'yancin bin addinai. Ban da wannan kuma, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ba da sanarwar cewa, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar John Sullivan zai kira taro kan batun Xinjiang a yau Talata.

Game da wannan batu, kakakin tawagar kasar Sin ya bayyana cewa, MDD muhimmin dandamali ne na kiyaye adalci a duniya. Amma abin bakin ciki shi ne, wai bisa hujjar kiyaye 'yancin bin addinai, Amurka ta yi fatali da abubuwa a zahiri, lamarin da ya sa aka kasa fahimta tsakanin fari da baki, har ma ta zargi wasu kasashe masu 'yanci ba tare da wata hujja ko dalili ba.

Kakakin ya kara da cewa, batun Xinjiang ba batu ne da ya shafi kalibu, addini, ko hakkin dan Adam ba, a maimakon haka, batu ne da ya shafi yaki da nuna karfin tuwo da ta'addanci. Jakadun kasa da kasa, da jami'an kungiyoyin duniya, da ma 'yan jaridu, kusan dubu daya sun ziyarci Xinjiang bi da bi, dukkansu sun kalli yadda Xinjiang ta samu kyawawan sakamako a fannin rigakafin abkuwar lamuran ta'addanci da kau da tsattsauran ra'ayi. Kuma sun fahimci cewa, abin da Xinjiang ke yi ya ba da muhimmiyar gudummawa ga sha'anin yaki da ta'addanci a duniya, a maimakon take 'yancin mazauna wurin na bin addini. Gaskiyar magana, wannan shi ne ainihin batun Xinjiang, babu wanda zai shafa wa kasar Sin kashin kaji.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China