Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labarai na yammacin duniya suna da hannu wajen bata yanayin Hong Kong
2019-11-15 13:35:55        cri
Kwanan baya, kafofin watsa labarai na yammacin duniya da suka hada da BBC, CNN da kuma jaridar The New York Times sun fara watsa labarai game da tashe-tashen hankula dake faruwa a yankin Hong Kong na kasar Sin. Haka kuma sun watsa rahotanni game da masu tada kayar baya kan yadda suka cinna wuta a makarantu, da kaiwa fararen hula hare-hare da kuma jefa kayayyaki daga sama don gurgunta harkokin zirga-zirga da dai sauransu, amma a baya sun bayyana cewa, wadanda suka aikata wadannan danyen aiki, ba sa dauke da makamai, wai sun yi haka ne domin neman dimokuradiyya.

Amma duk wanda ya san gaskiyar magana, ya san cewa, wadannan kafofin watsa labarai na yammacin duniya suna da hannu wajen bata yanayin Hong Kong, da kuma haddasa asarar dukiyoyi da tashe-tashen hankula a yankin, domin ba sa fadan gaskiyar abin da ke faruwa, maimakon haka, suna goyon bayan masu tada kayar baya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China