Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tattauna kan raya yankin musamman na Guangdong, Hong Kong and Macao
2019-11-13 21:30:07        cri
An kaddamar da shirin raya yankin musamman na Guangdong, Hong Kong and Macao a watan Faburairun bana. A yayin babban taro game da yankin karo na farko da aka shirya a jiya Talata, masu masana'antun Hong Kong da Macao sun bayyana cewa, raya yankin ya samar da sabuwar damar ci gaba ga yankunan uku.

Baya ga haka, sun bayyana cewa, a 'yan kwanakin da suka wuce, kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bullo da wasu manufofi da matakan nuna gatanci ga yankunan Hong Kong da Macao, don ganin aikin raya gundumar ya kai ga samar da alheri ga jama'a, musamman ma matasa. A cewarsu za su yi amfani da fifikonsu don hada kai tare da sauran biranen dake yankin, da nufin samun ci gaba tare. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China