Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rikici na kara kamari a HK, inda masu zanga-zanga ke kai hari kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba
2019-11-15 11:12:34        cri

Masu zanga-zanga a yankin musamman na HK na kasar Sin na ta kai hari kan mazaunan da ba su ji ba, ba su gani ba, wadanda ba su goyi bayan ayyukansu ba, inda har suka cinna wa wani mutum wuta, wadda alama ce dake nuna cewa, rikicin da ake ci gaba da yi, ya kara munana.

A ranar Laraba, wani mai aikin tsaftace muhalli mai shekaru 70 ya ji mummunan rauni, bayan dutsen da masu zanga-zanga ke jefa da shi ya same shi a ka, lamarin da ya auku a yankin dake kusa da tashar jirgin kasa ta Sheung Shui.

Yayin wani taron manema labarai, rundunar 'yan sandan yankin ta ce an gano da yawa daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin.

Rundunar ta ce mutumin da masu zanga-zangar suka cinnawa wuta a ranar Litinin, na fama da kuna irin na mataki na 2 a kaso 50 na sassan jikinsa, kuma har yanzu yana cikin mummunan yanayi a asibiti.

Shi kuma wani mutum mai shekaru 57 da ya yi rigima da wani daga cikin masu zanga-zangar bisa bambancin ra'ayin siyasa a yankin Ma On Shan, an masa dukan kawo wuka tare da cinna masa wuta.

Masu zanga-zangar sun kai hare-hare a sassa daban daban na yankin HK a ranar Laraba, inda suka kawo tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa a tituna da bugun masu wucewa da kuma lalata kayayyaki.

Yayin samamen da 'yan sanda suka kai a ranar Larabar, sun tsare mutane 224 bisa laifukan gudanar da zanga-zanga ba bisa doka ba da mallakar makamai da cinna wuta. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China