Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin kwamishinan ma'aikatar harkokin wajen Sin a yankin musamman na Hong Kong ya yi kira a kawo karshen tashin hankalin dake faruwa a yankin
2019-11-12 20:36:01        cri
Ofishin kwamishinan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin musamman na Hong Kong (HKSAR), ya yi Allah wadai da ma adawa da kalaman baya-bayan nan da ma'aikatar harkokin wajen Amurka da ofishin harkokin wajen Birtaniya da na kasashe renon Ingila da wasu 'yan siyasar kasashen biyu suka yi, inda suka jirgika gaskiya tare da kasa bambancewa tsakanin gaskiya da karya.

Mai Magana da yawun ofishin kwamishinan, ya bayyana cewa, a 'yan kwanakin nan, masu bore da suka sanya ruguna masu launin baki, sun tayar da rikici, inda suka barnata dukiyoyi da haddasa tashin hankali a sassan yankin na Hong Kong, da jefa bama-baman da aka hada da fetur cikin jiragen karkashin kasa dake aiki, da ma duka tare da cinnawa mutane wuta da ransu saboda bambancin ra'ayoyi.

Kakakin ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, irin wannan danyen aiki, ba shi da bambanci da ta'addanci, ya kuma wuce mizanin gangamin lumana da ma 'yancin fadin albarkacin baki, ya shiga wani rukunin rashin da'a.

Kakakin ya kara da cewa, wasu 'yan siyasar Amurka da Burtaniya, sun juya kokarin 'yan sanda na dawo da doka, da dakatar da tashin hankalin da masu bore suka tayar da ayyukan rashin Imani da suka aikata, wanda ya sake tabbatar da cewa, suna hada baki tare da goyon bayan masu tayar da tashin hankalin. Yana mai cewa, mazauna yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin da ma al'ummomin kasashen duniya, ba za su lamunci irin wadannan munanan ayyuka ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China