Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Sin sun tattauna da wakilan kasa da kasa kan batun Xinjiang da Hong Kong a MDD
2019-10-25 10:02:24        cri

Kwanan baya, zaunannen tawagar kasar Sin dake MDD da kungiyar nazarin hakkin Bil Adama ta kasar Sin sun gudanar da wani taron karawa juna sani a New York, hedkwatar MDD, inda suka gayyaci masana na kungiyar nazarin hakkin Bil Adama ta kasar Sin da na kungiyar ingiza tuntubar kasa da kasa da su yi musanyar ra'ayi da wakilan zaunannun tawagogin kasa da kasa dake MDD kan matakin da Sin take dauka na kawar da tsattsauran ra'ayi a yankin Xinjiang da kuma gyaran fuska da aka yiwa dokar yankin Hong Kong, taron dai ya samu halartar wakilan kasashen Pakistan, Cuba, Venezuela, Koriya ta arewa, Belarus, Nicaragua, Saudi Arabia, Indonesiya, Vitnam, Burundi, Laos da Singapore da Kamuru.

Jami'an wadannan kasashe sun bayyana cewa, sun kara fahimtar batun yankunan Xinjiang da Tibet da kuma Hong Kong, kuma suna ganin cewa, hakikanin halin da ake ciki a wadannan wurare ba kamar labaran da kafofin yada labarai na kasashen yamma ke bayarwa ba, sun kara da cewa, ta'addanci babbar barazana ce ga duk Bil Adama, kuma wajibi ne a gudanar da aikin yaki da ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi a Xinjiang. Kuma aikin tada zaune tsaye da masu bore suka gudanar a Hong Kong na girgiza duk duniya, ana sa ran a kwantar da hankalin wuri tun da wuri. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China