![]() |
|
2019-11-10 19:59:15 cri |
Shirin talabijin din dai babban kamfanin talabijin da radio na kasar Sin (CMG) ne ya kirkire shi, ya kuma kaddamar da shi a ranar 10 ga watan Nuwamba ta wasu kafafen watsa shirye shirye masu tasirin gaske. A kasar ta Girka ma manyan tashoshin watsa labarai na "The sky media" da kamfanin dillancin labarai na "Athens-Macedonian" sun watsa wannan shiri, yayin da kuma sauran kafofin sadarwa na yanar gizo suka yada shi kai tsaye. Haza za lika an kaddamar da shafin sada zumunta na kamfanin CMG na Sin samfurin kasar ta Girka a dai wannan rana.
Shi dai wannan shiri na kunshe ne da labarai game da yadda Sin ta samu sauye-sauye cikin shekaru 70 na ci gaban ta. (Ma'aikacin sashen Hausa: Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China