Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya isa Girka domin fara ziyarar aiki
2019-11-11 09:14:31        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa kasar Girka a jiya Lahadi, domin fara ziyarar aiki ta yini 3, a wani mataki na karfafa abota da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu. Wannan ce dai ziyarar farko da wani shugaban kasar Sin ya kai kasar cikin shekaru 11.

Da yake tsokaci game da ziyarar, shugaba Xi ya ce cikin shekarun baya bayan nan, Sin da Girka suna daukar manyan matakan inganta dangantakar su, idan aka yi la'akari da yawan ziyarar juna da manyan jami'an kasashen ke kaiwa juna, da zurfafa amincewa da juna ta fannin siyasa tsakanin su, da nasarar da ake samu daga shawarar ziri daya da hanya daya, wadda ta bayyana karara, a aikin tashar jiragen ruwa ta Piraeus.

Kaza lika kasashen biyu na ci gaba da tattaunawa da juna, da aiwatar da tsare tsare game da batutuwa da suka jibanci kasa da kasa da na shiyya shiyya, wanda hakan ya taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da daidaito, da ci gaba, da wadata a duniya baki daya.

Ya ce, yana fatan shi da shugaban Girka Prokopis Pavlopoulos, da firaministan kasar Kyriakos Mitsotakis, za su yi musayar ra'ayi game da matakan bunkasa hadin gwiwar kasashen su a sabon yanayi da ake ciki, ta yadda za a kai ga fitar da sahihin tsarin aiwatar da karin hadin gwiwa a nan gaba, da bude sabon babin kawance bisa dukkanin fannoni tsakanin kasashen biyu. (saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China