Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin: Alakar Sin da Uzbekistan ta shiga wani muhimmin lokaci dake bunkasa cikin sauri
2019-11-01 20:36:43        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana a yau Jumma'a cewa, alakar kasarsa da Uzbekistan a shekarun baya-bayan nan, ta shiga wani lokaci mai muhimmanci inda ta ke bunkasa cikin sauri, karkashin ka'idojojin da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

Li ya bayyana hakan ne, yayin da ya isa Uzbekistan don halartar taron firaministocin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 18 da gudanar da ziyarar aiki a kasar.

Ya bayyana cewa, yana fatan yin musayar ra'ayoyi da shugabannin Uzbekistan, kan yadda sassan biyu za su zurfafa alaka a fannoni daban-daban, ta yadda za a daga matsayin alakar Sin da Uzbekistan bisa manyan tsare-tsare zuwa gaba da yadda za ta amfani al'ummomin kasashen biyu.

Li ya yi nuni da cewa, yayin da duniya ke fuskantar yanayi mai sarkakiya, kungiyar SCO tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a shiyyar da karfafa samar da ci gaba da makoma mai kyau ga kasashe mambobinta.

Ya ce, yana fatan yin musayar ra'ayoyi da dukkan bangarori game da yadda za a aiwatar da matsayar da aka cimma a taron kolin Bishkek a watan Yuni da ma yadda za a bunkasa kungiyar gami da alakar bangarori dabam-daban. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China