Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya yi alkawarin kasancewar bangarori daban daban a ganawarsa da Guterres
2019-11-04 09:58:21        cri

Gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga mu'amalar bangarori daban daban a harkokin da suka shafi batutuwan kasa da kasa, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yayin ganawarsa da babban sakataren MDD Antonio Guterres a ranar Lahadi.

Ya ce, kasar Sin, a matsayinta na mambar dindindin a kwamitin sulhun MDD, za ta ci gaba da kiyaye tsarin kasancewar bangarori daban daban, da gudanar da harkokin kasa da kasa karkashin manufofin MDD, da kuma goyon bayan dokokin kasa da kasa karkashin tsarin doka da oda na duniya.

Mista Li ya ce, kasar Sin a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da MDD, da yin aiki tare da dukkan bangarori, da nufin cimma nasarar ajandar samar da dawwamamman ci gaba na MDD nan da shekarar 2030.

A nasa bangaren, Guterres ya ce, tilas ne kasashen duniya su guji aikata duk wasu abubuwan da za su kawo rarrabuwar kawuna da samar da wani tsari iri biyu da kafa wasu dokoki na kashin kai.

Ya ce hakika ci gaban kasar Sin na lumana ne kuma mataki ne na kara dunkulewar bangarori daban daban na duniya, kuma zai kara kiyaye zaman lafiyar duniya baki daya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China