Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakiyar firaministan Sin ta ziyarci Ghana
2019-11-12 14:06:46        cri
Daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga wata, mataimakiyar firaministan kasar Sin Sun Chunlan ta kai ziyarar aiki kasar Ghana, inda ta gana da shugaban kasar Akufo-Addo, da kuma yin shawarwari da mataimakin shugaban kasar Mahamudu Bawumia.

Sun Chunlan ta ce, shekara mai zuwa shekara ce ta cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Ghana, tana mai cewa ya kamata kasashen biyu su karfafa mu'amalar dake tsakaninsu kan neman ci gaban kasa da kuma gudanar da harkokin kasa. Haka kuma, ya kamata a zurfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Ghana bisa hadin gwiwar da za su yi wajen gudanar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" da dandalin tattaunawar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka.

Bugu da kari, ta ce, a halin yanzu, kasar Sin tana dukufa wajen kara bude kofa ga waje, ya kamata kasar Ghana ta yi amfani da wannan dama wajen habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin raya kasuwanni, zuba jari da kuma neman karuwar tattalin arziki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China