Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon shugaban Ghana ya yabawa kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa ga ci gaban Ghana
2019-08-17 15:07:18        cri
Tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya yabawa kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa wajen bunkasa ci gaban kasar ta Ghana.

Da yake zantawa da Wang Shiting, jakadan kasar Sin a Ghana, Mahama, ya yabawa gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa wajen taimakon da suke bayarwa na gudanar da muhimman ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa iri daban daban a kasar.

Mahama ya ce, muhimman ayyukan raya kasar da Ghana ta ci gajiyarsu sun hada da jami'ar kiwon lafiya da nazarin kimiyya, da aikin gina tashar samar da iskar gas ta Atuabo, da kuma guraben karo ilmi da gwamnatin Sin ta baiwa 'yan kasar Ghana masu yawan gaske wadanda suka samu damar halartar karatu a muhimman fannonin raya ci gaban kasa a kasar Sin.

Tsohon shugaban na Ghana ya ce, ya yi amanna Ghana da Sin za su ci gaba da cin moriyar kyakkyawar huldar dake tsakaninsu domin amfanawa al'ummomin kasashen biyu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China