Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin StarTimes ya kuduri niyyar sauya tsarin noma a Afrika
2019-09-07 16:02:48        cri
Kamfanin StarTimes na kasar Sin, mai yada shirye-shiryen talabijin, ya yi alkawarin kara shiga nahiyar Afrika, domin tallafawa wajen sauya tsarin noma a nahiyar.

Shugaban kamfanin Startimes a Nijeriya, Zhang Junqi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kamfanin da ake biya domin samun shirye-shiryensa na talabijin, zai yi amfani da dandalinsa na zamani wajen yada bayanai.

Ya ce ta hakan, kamfanin na Startimes zai kwatanta abun da aka yi a kasar Sin, inda harkokin noma ke samun ci gaba cikin sauri, ta hanyar ware tasoshin talabijin musamman domin yada harkokin noma da koyar da manoma yadda za su noma abinci da sauran tsirrai domin bunkasa ayyukansu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China