Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana ta yi kira da a hada hannu wajen kare hakkokin yara
2019-06-12 11:02:00        cri

Ma'aikatar kula da jinsi da yara da kare al'umma ta kasar Ghana MGCSP, ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da iyaye da malamai da shugabannin al'umma dake kula da yara, su hada kai wajen kare yaran.

Wata sanarwa da aka fitar domin ranar yaran Afrika na bana mai taken: "Ayyukan jin kai a Afrika: hakkin yara shi ne farko", ma'aikatar da abokan huldarta sun bukaci dukkan jama'a su hada hannu wajen tabbatar kare hakkokin yara ko da ana tsaka da fuskantar rikici jin kai.

Sanarwar ta ce, a matsayin kasa, akwai bukatar inganta zaman lafiya a cikin al'ummomi ta hanyar martaba hakkokin dukkan yara, kamar yadda yarjejeniyar MDD kan hakkokin yara ta tanada yayin da take cika shekaru 30.

Kasashe mambobin Tarayyar Afrika da abokan huldarsu, na bikin ranar yaran Afrika ne a ranar 16 ga watan Yuni na kowacce shekara, tun daga shekarar 1991, domin tunawa da zanga-zangar Soweto na kasar Afrika ta Kudu a shekarar 1976.

Dalibai bakaken fata sun yi zanga-zanga ne domin nuna adawa da tsarin ilimi da fararen fata suka gabatar, lamarin da ya kai ga 'yan sanda kisan daliban masu zanga-zangar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China